28 Mayu 2022 - 15:03
​Kasar Saudia Da Isra’ila Suna Dab Da Samar Da Huldar Jakadancin A Tsakaninsu

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Saudia sun bayyana cewa wata tawagar manya-manyan jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ziyarci birnin Riyad na kasar Saudia a cikin makon da ya gabat.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Channel 12 ta HKI yana cewa tawagar ta gana da jami’an gwamnatin kasar Saudia inda suka tattauna batutuwa da dama daga cikin har da batun tsaro a gabas ta tsakiya, da kuma aiki tare a wannan bangaren.

Kafin haka a shekarar da ta gabat tsohon firai ministan haramtacciyar kasar Benyamin Natanyahu ya je birnin Riyar inda ya gana da Muhammad bin salman yarima mai jiran gadon sarautar kasar.

Wasu masana sun bayyana cewa suna ganin samar da hulda tsakanin kasashen biyu ya zama nan kusa, bayan da aka dade ana boye dangantaka dake tsakanin kasashen biyu.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta jagoranci abinda ta kira sulhun Ibrahimiyya a tsakanin kasashen UAE, Bahrain, Morocco da kuma Sudan, da HKI.

Da alamin gwamnatin kasar Saudiya zata samar da huldar jakadanci da HKI, wacce ta dade tana cewa zata yi hakan.

342/